Wednesday, March 19, 2025

Falala da alamomin daren lailatul Qadr

Falalar daren lailatul kadr

Daren lailatul kadr dare ne dake da matukar Falala ga Musulmi saboda da a cikinsa ne Allah Madaukakin sarki ya fara saukar da Alkur'ani mai girma daga baitul izza zuwa duniya ta hanyar wahayi ga fiyayyen Halittarsa Annabi Muhammad (S.A.W).

Allah Madaukakin sarki ya kwadaitar da musulmai tarin ladar da ake samu ga duk Wanda yayi wata ibada a cikin Daren Inda yake cewa a cikin Alkur'ani mai tsarki a surah kadr, (Suratul Qadr 97:3)

" الْقَدْرِ خَيْرٌ مِنْ أَلْفِ شَهْرٍ"

Daren Lailatul Qadri ya fi wata dubu alheri (wato bautar Allah a cikin wannan dare ya fi falala da bauta masa watanni dubu, watau shekara 83 da wata 4).

Duk da cewa Allah Madaukakin sarki bai sanar da lokacin da Daren lailatul kadr ke faruwa ba, Amma Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi ya bamu haske game da yadda zamu iya riskan wannan daren Mai dunbin Falala kamar yadda yazo a cikin hadisin da Nana Aisha (RA) ta ruwaito. Inda yake cewa: 

 "Ku nemi daren lailatul qadari a cikin dararen mara na goman karshen watan Ramadan." 
[Sahihul Bukhari 2017]

Abubuwan da aka so Musulmi su yawaita yi domin neman dacewa da wannan daren na lailatul kadr.
Anso a yawaita addu'a a goman ƙarshe na watan Ramadan, musamman ma a wadannan kwanakin na mara  (21-23-25-27-29) da ake tsammanin faruwar daren lailatul kadr a cikinsu, haka zalika ana so mutum ya kara tsanantawa a wajen yin addu'o'i a dare da rana, da fatan samun karbuwarsu a wajen Allah mahalicci, da kuma neman falalarSa, gafaranSa, rahamarSa da kuma karamcinSa ga bayinSa (S.W.T).

Wasu daga cikin Alamomin daren lailatul Qadr 

Lailatul qadr na da alamomi da ake gane shi da su,Wadannan alamomi sukan kasance ne a cikin daren.

1-Dare Ne Matsakaici,Babu Zafi sosai Ko Sanyi sosai A Cikinsa

An karbo daga Jabir Dan Abdullahi Allah ya yarda da shi ya ce,
“Haqiqa ni an nuna min daren Lailatul Qadri,sannan an mantar da ni shi,yana goman qarshe na Ramadan, dare ne babu sanyi ko zafi a cikinsa, kuma mai haske ne, ba zafi ba sanyi (mai cutarwa a cikinsa
@Ibn Khuzaima ne ya rawaito shi.

2-Rana Tana Fitowa Da Safiyar Daren Fara Tas Ba Haske Tare Da Ita.

Yayin da aka tambayi Ubayyu Dan Ka’abu Allah ya yarda da shi a kan alamomin daren Lailatul Qadri, sai ya ce, (Alamar da Manzon Allah ( ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ) ya ba mu labari ita ce, rana tana bullowa a wannan rana babu haske tare da ita)
@Tirmizi ne ya rawaito shi.

2-Za ka iya ganinshi (Lailatul Qadr) a mafarki kamar Yadda sahabbai suka gani
@Ba wai za ai mafarkin wani tsunburkai ba ne a a za a iya yin mafarkin ga shi ana ibada a cikin daren za aji karsashi wajen yin ibadarsa

3-Yanayi zai canza ya zama mai dadi,Za a ji iska mai dadi, nutsattsiya.
@Ibn Khuzaima da Dayalisi

4-Samun Natsuwar zuciya da kimtsuwa,Farin ciki cikin zuciya da samun jin dadin ibada.

6-Rana zata fito ba zafi (in lokacin zafi ne)
@Muslim

Wadannan su ne alamomin da ake gane daren lailatul qadr. Amma da ake cewa itatuwa zasu fadi su yi sujada,zaka ga rana a kasa, karnuka za su daina kuka,za a ga taurari a kasa,wannan qage-qage da tatsuniya aka qaga a cikin addini wanda kuma ba gaskiya ba ne.

Allah ne mafi sani.

Allah ya bamu ikon ganin Daren lailatul kadr tare da sadar damu dukkan alkairan dake cikinsa don matsayin Annabi MUHAMMAD (S.A.W).




Article Translation in English Language.

Laylatul Qadr night is a very blessed night for Muslims because it was during it that Allah the Almighty sent down the Holy Qur'an from Baitul Izza to the world through revelation to His Most High Creator, Prophet Muhammad (S.A.W).

Allah, the Almighty, enlightened the Muslims about the reward that is available to all those who perform a prayer in the Night of qadr, where he says in the Holy Qur'an in Surah Qadr (Al-Qadr 97:3)

"The night of Al-Qadr (Decree) is better than a thousand months (i.e. worshipping Allah in that night is better than worshipping Him a thousand months, i.e. 83 years and 4 months)".

Even though Allah, The All mighty did not announce when the Night of Laylatul Qadr is happening, but the Prophet Muhammad, peace and blessings of God be upon him, gave us advice about how we can reach this night of blessings as mentioned in the hadith narrated by Nana Aisha (RA). Where He said:

"Search for the Night of Qadr in the odd nights of the last ten days of Ramadan." [Sahih Bukhari 2017]

There are many things that Muslims should do in order to be suitable for this night of Lailatul Qadr. 
It is important to pray more in the last ten days of Ramadan, especially in these odd days (21-23-25-27-29) in which the Night of Laylat al-Qadr is expected to occur, so a person should be more diligent in praying day and night, hoping to be accepted by Allah the Creator, and seeking His grace, His forgiveness, His mercy and His generosity to His servants, (S.W.T).

SHARE THIS

Author:

Etiam at libero iaculis, mollis justo non, blandit augue. Vestibulum sit amet sodales est, a lacinia ex. Suspendisse vel enim sagittis, volutpat sem eget, condimentum sem.

0 comments: