Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta buƙaci Musulman Najeriya da su yi koyi da kyawawan ɗabi’u da halayen Annabi Muhammad (S.A.W.) yayin bikin Eid-el-Maulud na shekarar 2026.
A cikin saƙonta ga al’ummar Musulmi, ta jaddada muhimmancin tausayi, yafiya da zaman lafiya waɗanda suka kasance daga cikin kyawawan halayen Annabi Muhammad (S.A.W.).
Ta kuma ƙarfafa Musulmi da su ci gaba da yaɗa zaman lafiya a gidajensu, al’ummominsu da kuma faɗin Najeriya.
Mrs. Remi ta bayyana fatan cewa bikin Mauludin zai ƙara ƙarfafa haɗin kai da zaman lafiya, tare da kawo sabon fata, albarka da kwanciyar hankali ga al’ummar Najeriya.
Tags
Labaran Duniya
