Monday, July 6, 2026

An Kai Gawar Marigayi Tsohon Jagoran Addinin ƙasar Iran Ayatullah Ali Khamenei Birnin Qom Domin Ci Gaba da Jana'iza.

An Kai Gawar Marigayi Tsohon Jagoran Addinin ƙasar Iran Ayatullah Ali Khamenei Birnin Qom Domin Ci Gaba da Jana'iza.

An kai gawar marigayi Jagoran Addinin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Ayatullah Ali Khamenei, zuwa birnin Qom domin ci gaba da gudanar da bukukuwan jana'izarsa kafin a binne shi.

A cewar kafafen yaɗa labaran gwamnatin Iran, an ɗauko gawar ne da jirgin sama mai saukar ungulu daga Tehran bayan miliyoyin mutane sun cika titunan babban birnin na tsawon kwanaki uku suna yi masa bankwana.

Ayatullah Ali Khamenei da mutum huɗu daga cikin iyalansa sun rasu ne sakamakon wani harin sama da kawance Amurka da Isra'ila suka kai a ranar 28 ga Fabrairu.

Miliyoyin masu makoki sanye da baƙaƙen kaya ne suka hallara a Tehran, inda suke watsa furanni kan akwatunan gawarwakin yayin da jerin gwanon jana'izar ya ratsa manyan titunan birnin. 
Kafafen gwamnatin Iran sun bayyana taron a matsayin ɗaya daga cikin mafi girma a tarihin ƙasar.

Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, da manyan jami'an gwamnati da shugabannin soji da sauran manyan jami'ai sun halarci jana'izar. Tsohon shugaban ƙasar, Mahmoud Ahmadinejad, shi ma ya bayyana a bainar jama'a bayan shafe lokaci ba a ganinsa.

Sai dai magajin Khamenei kuma ɗansa, Mojtaba Khamenei, bai bayyana a wurin jana'izar ba. Masana sun ce matsalolin tsaro da kuma tsagaita bude wutar yaƙin da ke tsakanin Iran da Amurka da Isra'ila ne suka hana shi fitowa fili.

Hukumomin Iran sun ce sama da mutum 34,000 sun samu kulawar lafiya yayin bukukuwan jana'izar, ba tare da samun rahoton rasuwar kowa ba.

Ana sa ran za a kammala bukukuwan jana'izar a ranar Alhamis da binne Ayatullah Ali Khamenei a garinsu na Mashhad, inda ake sa ran dubban masu makoki za su sake hallara.

0 Comment about the Post: