Friday, June 26, 2026

Tsohon Jami’in Amurka Ya Ce yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) tsakanin Iran da Amurka Nasara Ce Ga ƙasar Iran.

Tsohon Jami’in Amurka Ya Ce yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) tsakanin Iran da Amurka Nasara Ce Ga ƙasar Iran.

Wani tsohon jami’in Amurka kuma masani, Matthew Hoh, ya bayyana cewa yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) tsakanin Iran da Amurka wata babbar nasara ce ta siyasa ga Tehran, yana mai cewa Washington ta kasa cimma manufofinta ta hanyar matsin lamba na soja.

Hoh, wanda ya taba zama jami’in Sojin Ruwa na Amurka da kuma ma’aikacin Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, ya ce yarjejeniyar ta nuna cewa Iran ta iya tinkarar matsin lamba daga Amurka da kawayenta tare da tilasta komawar tattaunawa.

Ya bayyana cewa rangwamen da Amurka ta yi ya ba masu sharhi mamaki, domin da yawa daga cikinsu ba su yi tsammanin rikicin zai kare da irin wannan sakamako ba.

A cewarsa, matsin tattalin arziki da rikicin ya haifar ya jefa kasuwar makamashi ta duniya cikin fargaba, lamarin da ya sa Amurka ta koma hanyar diflomasiyya.

Hoh ya ce ya kamata Iran ta yi amfani da wannan damar wajen samun tabbaci da moriya na dogon lokaci daga duk wata yarjejeniya ta karshe.

Sai dai ya yi gargadin cewa ana iya sake samun sabbin takaddama a nan gaba, saboda har yanzu manufar Amurka kan Iran ba ta da tabbas.

0 Comment about the Post: