Sheikh Halliru Maraya ya yi Takaitaccen Bayani game da falalar Maulin ANNABI MUHAMMAD (S.A.W), inda ya baiyana cewa muhimmacin Maulidi bashi da iyaka Kuma Duk Wanda yayi Maulidin ANNABI MUHAMMAD Sallallahu Alaihiwasallam to hakika yayi koyi ne da SHI (S.A.W), domin ANNABI ne ya fara girmama Ranar da aka haife Shi.
Saboda ANNABI (S.A.W) ya bayyana cewa Litinin ce ranar da aka haife Shi, shi yasa ya ke yin azumi a wannan ranar, Don haka Maulidi ba bidi'a ba ne.
Sannan Kuma Maulidi nuna girmamawa ne ga Janibin ANNABI (S.A.W).
Inda ya kara da cewa za'a iya yin duk wani abun da shari'a ta yarda da shi a matsayin Maulidi, kamar yin Karatun Alkur'ani da karantar da halayen ma'aiki (S.A.W) ko tallafawa wa marayu da marasa lafiya.
Daga karke ya kara da cewa ba'a yarda mutum ya aikata dukkan wani abu da shari'a tayi hani da shi ba a matsayin Maulidin ANNABI MUHAMMAD Sallallahu Alaihiwasallam.
Saurari Takaitaccen Bayani game da falalar Maulidi daga bakin Shieikh Halliru Maraya.
_2.jpeg)
0 comments: