Thursday, November 28, 2024

Adadin yawan kwanakin Jinin haila (Jinin A'ada)

 Adadin yawan kwanakin Jinin haila (Jinin A'ada)

Mafi ƙarancin kwanakin jinin haila ba su da iyaka.
Wato, yana iya yiwuwa mace ta ga jini na ɗan lokaci kaɗan—kamar awa ɗaya, mintuna kaɗan, ko kwana ɗaya—sannan ya dauke. Haka kuma yana iya kaiwa har zuwa kwana goma sha biyar (15). Amma mafi yawan kwanakin haila ba su wuce kwana goma sha biyar (15); duk abin da ya wuce haka, ba jinin haila ba ne, sai dai jinin istihala (jinin cuta).

MAFARIYA (Sabuwar mai haila)

Mafariya ita ce mace da ta fara ganin jinin haila a karon farko.

A wannan yanayin, za ta lura da kwanakin da jinin yake fitowa.

Idan ta ga jini ya tsaya bayan kwana 1, ko 2, ko 3, ko 4, ko 5, har zuwa 15, kuma bai sake dawowa ba, to sai ta yi wanka (ghusl) ta tsarkaka.

Amma idan jinin ya ci gaba har ya wuce kwana goma sha biyar (15), to sai ta yi wanka, domin jinin ya koma istihala (jinin cuta), sannan ta ci gaba da ibadunta kamar yadda ya dace.

Allahu A’alam.

SHARE THIS

Author:

I am a personal blogger by experience, interesting in creativity, learning new things and sharing Islamic contents for the benefit of Muslim ummah.

0 comments: