Sunday, August 16, 2026

An Zaɓi Dakta A’isha Mustapha Shugabar Ƙungiyar Likitoci na jihar Kaduna.
An Zaɓi Dakta A’isha Mustapha Shugabar Ƙungiyar Likitoci na jihar Kaduna.

An zaɓi Dakta A’isha Mustapha a matsayin sabuwar Shugabar Ƙungiyar Likitocin Nijeriya (NMA), reshen Jihar Kaduna, bayan gudanar da zaɓen ƙungiyar a makon da ya gabata.

Dakta A’isha ƙwararriyar likita ce a fannin mata da haihuwa (Obstetrics and Gynaecology), kuma ta samu nasarori da dama a fannin aikin likita, ilimi da hidimar kiwon lafiya.

Kafin samun wannan matsayi, Dakta A’isha ta samu lambobin yabo da karramawa daban-daban, ciki har da karramawa daga Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, a wajen ƙaddamar da shirin PECCIN Launch 2025.

A shekarar 2024, ta kuma samu Certificate of Excellence in Peer Reviewing daga Global Academy Publisher, yayin da a shekarar 2023 ta samu Impact Award daga Ovarian Cancer Coalition.

A fannin ilimi, Dakta A’isha ta yi fice sosai. A shekarar 2015, ta zama ɗalibar da ta fi ƙwarewa a jarabawar WACS Part I a fannin Obstetrics and Gynaecology. Haka kuma, ɗaliban likitanci na Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, sun ba ta lambar yabo ta Mafi hazakar Malama a shekarun 2016 da 2017.

Ta kuma kammala karatunta a matsayin mafi hazakar ɗaliba a fannin Obstetrics and Gynaecology a Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, a shekarar 2008.

A matsayinta na sabuwar shugabar NMA ta Kaduna, Dakta A’isha ta ce za ta mayar da hankali wajen kare haƙƙin likitoci, tabbatar da aiwatar da albashi da alawus-alawus na CONMESS, inganta walwalar likitoci da samar da tallafin lafiyar ƙwaƙwalwa.

Ta kuma bayyana cewa za ta yi aiki wajen inganta inshorar lafiya, lokutan aiki, kariyar shari’a ga likitoci da samar da ƙarin damar horaswa da bunƙasa ƙwarewar ma’aikatan lafiya.

Dakta A’isha, wadda ’yar asalin Jihar Kano ce, ta yi makarantar firamare a Hotoro, sannan ta halarci Federal Government College Kano kafin ta shiga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

A halin yanzu tana aiki a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABUTH), Shika, kuma ta halarci ƙasashe daban-daban domin ƙarin ilimi da ƙwarewa.

Kafin zaɓenta a matsayin shugabar NMA Kaduna, ta taɓa zama shugabar Ƙungiyar Likitoci Mata ta Nijeriya, reshen Kaduna, sannan ta riƙe muƙamin Sakatariyar NMA ta Jihar Kaduna.

Dakta A’isha ta gode wa abokan aikinta bisa amincewar da suka nuna mata, tare da yin alƙawarin shugabanci cikin gaskiya, adalci da rashin nuna bambanci.

Ta kuma yi kira ga likitoci da su haɗa kai domin ci gaban ƙungiyar da kuma inganta harkokin kiwon lafiya a Jihar Kaduna da Nijeriya baki ɗaya.

Tuesday, August 11, 2026

An Kashe Shugaban Leken Asirin Sojin Gabashin Libya a Harin Bam a Mota.
An Kashe Shugaban Leken Asirin Sojin Gabashin Libya a Harin Bam a Mota.

An kashe Manjo-Janar Fawzi al-Mansouri, shugaban hukumar leken asirin soji ta rundunar da ke iko da gabashin ƙasar Libya, bayan da aka kai masa harin bam a birnin Benghazi.

Rahotanni sun ce an dasa wata na’urar fashewa a cikin motarsa, inda aka tayar da ita yayin da al-Mansouri ke shiga motarsa a wajen gidansa da ke yankin Hawari a daren ranar Litinin.

Firaministan gwamnatin gabashin Libya, Osama Saad Hammad, ya yi Allah-wadai da kisan tare da yin alkawarin gudanar da bincike domin gano wadanda suka shirya da kuma wadanda suka aikata harin.

Hammad ya bayyana harin a matsayin “mummunan aikin ta’addanci da cin amana”, yana mai cewa ba za a bar wani mutum ya samu mafaka ba idan yana da hannu wajen tsarawa ko aiwatarwa ko daukar nauyin kudi ko kuma tunzura ayyukan kisan gilla da ta’addanci.

An nada al-Mansouri a matsayin daraktan leken asirin soji a Benghazi a shekarar 2024, tare da ba shi mukamin Manjo-Janar.

Kisan na zuwa ne yayin da Libya ke ci gaba da fama da rikicin siyasa da matsalolin tsaro, inda gwamnatoci masu hamayya da kungiyoyin masu dauke da makamai ke ci gaba da samun tasiri duk da yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta shekarar 2020.

Libya ta rabu gida biyu tun daga shekarar 2014, bayan rikicin siyasa da na soji da ya biyo bayan juyin mulkin shekarar 2011 wanda ya kifar da mulkin tsohon shugaban kasar Muammar Gaddafi.

Rundunar LNA karkashin jagorancin Khalifa Haftar ce ke iko da manyan sassan gabashi da kudancin Libya, kuma tana da alaka da hukumomin da ke birnin Benghazi.

A gefe guda kuma, gwamnatin hadin kan kasa da duniya ke amince da ita, wadda ke da hedikwata a Tripoli, ita ce ke iko da mafi yawan yankunan yammacin kasar.

Kisan babban jami’in leken asirin sojin ya kara jefa haske kan matsalolin tsaro da Libya ke fuskanta, tare da haifar da sabbin damuwa game da makomar zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

Monday, August 10, 2026

Girgizar Ƙasa Mafi Ƙarfi Cikin Shekaru 10 Ta Hallaka Mutane 111 a Colombia.
Girgizar Ƙasa Mafi Ƙarfi Cikin Shekaru 10 Ta Hallaka Mutane 111 a Colombia.

Akalla mutane 111 ne suka rasa rayukansu, yayin da gine-gine da dama suka ruguje bayan wata girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 7.4 ta afku a yammacin ƙasar Colombia a yau Litinin.

Hukumomi sun ce girgizar ƙasar ta afku ne kusa da San José del Palmar a yankin Chocó, mai tazarar kusan kilomita 400 daga yammacin babban birnin ƙasar, Bogotá. Hukumar Binciken Ƙasa ta Amurka (USGS) ta ce girgizar ta afku ne a zurfin kusan kilomita 107.

Masu aikin ceto na ci gaba da bincike a cikin gine-ginen da suka ruguje domin gano mutanen da suka makale a ƙarƙashin baraguzan gini. 
An kuma samu mutane da dama da suka jikkata, yayin da girgizar ta tilasta wa mazauna yankuna daban-daban barin gidajensu.

Hukumar Kula da Yanayin Ƙasa ta Colombia ta bayyana girgizar a matsayin mafi ƙarfi da aka samu a ƙasar cikin shekaru 10 da suka gabata.

Shugaban Colombia, Abelardo de la Espriella, ya ayyana dokar ta-ɓaci domin a gaggauta samar da kuɗaɗen tallafin farfaɗowa daga bala'in. Ya kuma ce zai ziyarci yankunan da girgizar ta fi shafa.

Shugaban ya ce gwamnati ba za ta bar mutanen da abin ya shafa su kaɗai ba, tare da yin alkawarin cewa za a ba su dukkan taimakon da ake buƙata.

Bayan babbar girgizar ƙasar, an kuma samu wasu ƙananan girgizar ƙasa guda biyu masu ƙarfin 2.8 da 4.8.

Hukumomi sun dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a wasu filayen jiragen sama da suka haɗa da na Manizales da Quibdó da Armenia da Cartago da Buenaventura da Pereira.

A birnin Pereira, hotuna da bidiyoyin da kafafen yaɗa labarai na cikin gida suka wallafa sun nuna wani ɓangare na rufin filin jirgin sama yana faɗowa yayin da matafiya ke neman mafaka. An kuma ga mutane suna gudu a cikin wuraren da baraguzan gine-gine suka cika.

Yankin Chocó da ke bakin tekun Pacific na daga cikin yankunan da suka fi fama da talauci a Colombia. Yawancin yankunan karkara ne, kuma wasu wurare ba sa da sauƙin isa sai ta jirgin ruwa ko jirgin sama, lamarin da zai iya kawo cikas ga ayyukan ceto da tantance yawan asarar rayuka.

A babban birnin Bogotá, magajin birnin, Carlos Fernando Galán, ya ce babu rahoton mutuwar mutane ko munanan raunuka a birnin, sai dai wasu gine-gine sun samu tsagewa.

Colombia na fuskantar dubban ƙananan girgizar ƙasa a kowane wata, amma girgizar da ta kai ƙarfin maki 6.0 ko sama da haka ba kasafai take faruwa ba. 
A shekarar 1999, wata girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 6.2 ta afku a yankin noman kofi na ƙasar, inda ta hallaka sama da mutane 1,000.

Wannan bala'i ya zo ne makonni kaɗan bayan wasu manyan girgizar ƙasa sun afku a ƙasar Venezuela, inda aka ruwaito cewa fiye da mutane 6,000 sun mutu, yayin da daruruwan gine-gine suka lalace.

Saturday, August 8, 2026

An gano gawarwakin mutane 19 a ƙarƙashin baraguzan ginin Gaza
An gano gawarwakin mutane 19 a ƙarƙashin baraguzan ginin Gaza

Ma’aikatan agaji da rundunar kare fararen hula a Gaza sun gano gawarwakin Falasɗinawa 19, mafi yawansu mata da yara, a ƙarƙashin baraguzan wani ginin gidaje da ya rushe a Gaza.

A cewar Hukumar Kare Fararen Hula ta Gaza, an kammala aikin gano gawarwakin ne ranar Asabar, bayan shafe kwanaki huɗu ana gudanar da aikin bincike a ginin Karam da ke yammacin birnin Gaza.

Jami’ai sun ce aikin ceto da kwashe gawarwakin na fuskantar matsaloli saboda ƙarancin manyan injinan da ake buƙata wajen ɗaga manyan tarkacen siminti da suka ruguje.

A sakamakon haka, ma’aikatan kare fararen hula suna amfani da kayan aiki na yau da kullum da kuma ƙoƙarin hannu wajen neman gawarwakin mutanen da suka makale a ƙarƙashin baraguzan gine-gine.

Mohammed Abu Dan, wanda ke kula da ayyukan kwashe gawarwakin, ya ce bayan kammala aikin a ginin Karam, ƙwararrun ma’aikatan lafiya da jami’an kare fararen hula za su koma wani sabon wuri a Gaza City domin ci gaba da aikin neman waɗanda suka rasa rayukansu.

Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta ce akwai fiye da mutane 8,000 da har yanzu ake nema a ƙarƙashin baraguzan gine-gine a faɗin yankin.

Ta kuma bayyana cewa tun bayan fara aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a ranar 11 ga Oktoba na shekarar da ta gabata, an kashe aƙalla mutane 1,254, yayin da wasu 4,121 suka jikkata, sannan aka gano gawarwakin mutane 804 daga ƙarƙashin baraguzan gine-gine.

A cewar ma’aikatar, adadin mutanen da aka kashe tun bayan fara yaƙin a watan Oktoban 2023 ya haura 73,300, yayin da fiye da 174,000 suka jikkata.

Wannan aikin ceto ya zo ne kwanaki kaɗan bayan gudanar da jana’izar mutane 112 a birnin Gaza, waɗanda gawarwakinsu aka gano a ƙarƙashin baraguzan wani ginin gidaje da aka lalata a unguwar Sabra a watan Nuwamban 2023.

Thursday, August 6, 2026

Fadar Sarkin Gombe Ta Musanta Zargin Cewa Pantami Ya Taɓa Wulakanta Sarkin Gombe.
Fadar Sarkin Gombe Ta Musanta Zargin Cewa Pantami Ya Taɓa Wulakanta Sarkin Gombe.

Fadar Mai Martaba Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu-Abubakar III, ta musanta zargin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa an taɓa hana Sarkin ganawa da tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Dijital, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, lokacin da yake kan mukaminsa.

A cikin wata sanarwa, fadar ta bayyana zargin a matsayin ƙarya marar tushe, tana mai cewa an ƙirƙire shi ne saboda dalilan siyasa da nufin haifar da rudani tare da ɓata sunan masarautar.

Ajiya Masu Gombe, wanda ya yi magana a madadin fadar, ya ce Mai Martaba Sarkin Gombe da Farfesa Pantami sun daɗe suna da kyakkyawar alaƙa mai cike da mutunta juna.

Ya bayyana cewa zargin da ake yi cewa an hana Sarkin ganawa da Pantami ba gaskiya ba ne, yana mai jaddada cewa bai taɓa faruwa ba a tarihin hulɗar da ke tsakanin bangarorin biyu.

Fadar ta kuma yi kira ga jama'a da su guji yaɗa labaran ƙarya ko marasa tushe da za su iya zubar da mutuncin sarakunan gargajiya.

Haka kuma, ta gargadi masu ƙoƙarin jawo masarautu cikin siyasar ɓangaranci, tana mai cewa ya kamata a mutunta martabar sarakunan gargajiya tare da nesanta su daga rigingimun siyasa.

A ƙarshe, fadar ta bayyana cewa za ta ɗauki matakin shari'a kan duk wanda aka samu yana yaɗa ƙarya ko ɓata sunan Mai Martaba Sarkin Gombe da gangan.

Ta kuma buƙaci 'yan siyasa da magoya bayansu su gudanar da harkokinsu cikin ladabi da girmama cibiyoyin gargajiya.

Monday, August 3, 2026

Gobarar daji na ci gaba da addabar ƙasashen Faransa da Sifaniya.
Gobarar daji na ci gaba da addabar ƙasashen Faransa da Sifaniya.

Gobarar daji na ci gaba da addabar sassan ƙasashen Faransa da Sifaniya duk da cewa jami'ai sun bayyana cewa an fara shawo kan wasu daga cikin manyan gobarar da suka fi muni.

Dubban jami'an kashe gobara daga ƙasashen Turai na ci gaba da fafatawa da wutar domin hana ta bazuwa zuwa wasu yankuna, yayin da tsananin zafi da fari ke ƙara haɗarin barkewar sabbin gobara.

A kudu maso yammacin Faransa, musamman a yankunan Gironde da Var, gobarar ta ƙone dubban hekta na dazuka. Mahukunta sun ce babbar gobarar ƙasar mafi muni cikin shekaru da dama an shawo kanta, amma har yanzu ba a kashe ta gaba ɗaya ba.

Gobarar daji

A Sifaniya kuwa, gobarar da ta ƙone manyan yankuna kusa da Madrid ta ragu, lamarin da ya bai wa dubban mazauna da aka kwashe damar komawa gidajensu. Sai dai jami'an kashe gobara na ci gaba da yaƙi da wuraren da wutar ke sake tashi a lardunan Leon da Caceres.

Gobarar ta tilasta wa dubban mutane barin gidajensu, yayin da gidaje da sansanonin yawon buɗe ido da dazuka da sauran kadarori suka lalace sakamakon gobarar. Jiragen sama na kashe gobara yayin da jami'an agaji ke ci gaba da aiki domin dakile ragowar wutar.

Masana sun yi gargadin cewa nahiyar Turai, wadda ita ce ke saurin fuskantar hauhawar yanayin zafi fiye da sauran nahiyoyi, na ƙara fuskantar barazanar gobarar daji saboda ƙaruwar zafi da fari mai tsawo da kuma iska mai ƙarfi. 
Sun ce yanayin da ke haddasa gobarar daji a lokacin bazara ya ninka fiye da sau biyu idan aka kwatanta da farkon shekarun 1980.

Mahukunta sun buƙaci mazauna yankunan da ke cikin haɗari su kasance cikin shiri, saboda ana sa ran tsananin zafi zai ci gaba, lamarin da ka iya haddasa barkewar sabbin gobara a kwanaki masu zuwa.