Majalisar Dattawan Najeriya ta fara wani yunƙuri na kawo ƙarshen yadda wasu asibitoci ke ƙin karɓar marasa lafiya da ke buƙatar kulawar gaggawa, inda ta amince da wani kudirin doka da ke neman hukunta masu aikata hakan da tarar Naira 300,000 ko ɗaurin watanni shida a gidan yari.
Kudirin, wanda ya samu amincewar majalisar a karatu na biyu, na neman tilasta wa dukkan asibitocin gwamnati da masu zaman kansu a Najeriya ba da agajin gaggawa ga duk mara lafiyar da ya buƙaci hakan, ba tare da nuna bambanci ba.
Sanata Abdulaziz Musa Yar’Adua, mai wakiltar Katsina ta Tsakiya, ne ya ɗauki nauyin gabatar da kudirin, wanda ke neman yin gyara ga Dokar Lafiya ta Ƙasa ta 2014 domin ƙarfafa dokokin kula da marasa lafiya a lokacin gaggawa.
Idan aka amince da kudirin ya zama doka, babu wani asibiti ko ma'aikacin lafiya da zai samu damar ƙin ba mara lafiya agajin gaggawa saboda rashin kuɗi ko wasu dalilai.
Daga cikin muhimman abubuwan da kudirin ya ƙunsa akwai buƙatar asibitoci su fara tantance yanayin mara lafiya cikin mintuna 15 da isowarsa, sannan su fara matakan daidaita lafiyarsa cikin mintuna 30.
Haka kuma, an tanadi cewa ma'aikatan lafiya za su fara matakan ceton rai nan take idan sun gano cewa yanayin mara lafiya na barazana ga rayuwarsa. Waɗannan matakai sun haɗa da farfaɗo da numfashi, buɗe hanyoyin iska da kuma dakatar da zubar jini.
Kudirin ya kuma buƙaci asibitoci su samar da gadon kwantar da marasa lafiya cikin sa'o'i biyu idan akwai, yayin da waɗanda ba su da wurin kwantar da mara lafiya za su kasance wajibi su fara kula da shi tare da shirya masa hanyar zuwa wani asibiti.
Bugu da ƙari, dole ne asibitoci su kammala shirye-shiryen tura mara lafiya zuwa wata cibiyar lafiya cikin sa'o'i uku, sannan su samar da motar asibiti ko wata hanyar sufuri cikin mintuna 30 bayan yanke shawarar tura shi.
Haka kuma, kudirin ya tanadi horar da likitoci da sauran ma'aikatan lafiya kan hanyoyin ba da agajin gaggawa, tare da sabunta takardun shaidar ƙwarewarsu duk bayan watanni 18.
Da yake kare kudirin a gaban majalisar, Sanata Yar’Adua ya ce ana samun mace-macen da za a iya kauce wa a Najeriya sakamakon jinkirin samun kulawar lafiya da kuma rashin ingantattun hanyoyin tura marasa lafiya zuwa manyan asibitoci.
Ya bayyana cewa sabon tsarin zai tabbatar da cewa kowane ɗan Najeriya yana samun kulawar gaggawa ba tare da la'akari da matsayinsa na tattalin arziki, zamantakewa ko inda yake zaune ba.
Sanatan ya kuma yi nuni da cewa Najeriya na da kaso kusan kashi 10 cikin 100 na mace-macen mata masu juna biyu a duniya, inda ya ce jinkirin samun kulawar gaggawa na daga cikin abubuwan da ke ƙara ta'azzara matsalar.
Wasu sanatoci sun nuna goyon bayansu ga kudirin, ciki har da Sanata Mohammed Monguno da Sanata Diket Plang, waɗanda suka ce zai taimaka wajen rage mace-macen da ke faruwa sakamakon haɗurran mota da matsalolin haihuwa.
Sai dai Sanata Francis Faduyile ya yi gargaɗin cewa bai kamata a hukunta ma'aikatan lafiya ba tare da la'akari da halin da suke ciki ba, musamman ganin yadda wasu asibitoci ke fama da ƙarancin likitoci, kayan aiki da iskar oxygen.
Ya ce yana da wuya likita da ke kula da marasa lafiya da dama a lokaci guda ya iya cika dukkan ƙa'idojin lokacin da sabon mara lafiya ya shigo cikin gaggawa.
Shi ma Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Abba Moro, ya goyi bayan buƙatar yin gyara ga dokokin kiwon lafiya, inda ya jaddada cewa ceton rayukan mutane ya kamata ya kasance fifiko a duk lokacin da aka samu matsalar gaggawa.
Moro ya kuma yi Allah-wadai da yadda wasu asibitoci ke buƙatar rahoton 'yan sanda kafin su fara kula da waɗanda suka samu haɗarin mota, yana mai cewa irin wannan mataki na iya jinkirta ceton rayukan mutane.
A nasa ɓangaren, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bukaci sanatoci su goyi bayan ci gaba da nazarin kudirin, yana mai cewa akwai buƙatar haɗin gwiwar gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi wajen samar da ingantattun cibiyoyin lafiya.
Bayan amincewa da kudirin a karatu na biyu, an miƙa shi ga kwamitin majalisar mai kula da harkokin lafiya domin ƙarin nazari, inda aka ba shi makonni huɗu ya gabatar da rahotonsa.
Kudirin dai na da nufin tabbatar da cewa babu mara lafiya da zai rasa ransa saboda ƙin karɓarsa ko jinkirin ba shi agajin gaggawa a asibiti.
Tags
Labaran Duniya
