Wata Babbar Kotu a Jihar Kano ta yanke wa wasu mutane biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta same su da laifin hallaka wata mata mai suna Fatima Abubakar tare da ’ya’yanta shida a unguwar Dorayi Chiranci da ke birnin Kano.
Wadanda aka yankewa hukuncin sun hada da Umar Auwalu, wanda aka fi sani da Breaker, da Yakubu Dayyabu, wanda aka fi sani da Wawo.
Mai shari’a Nasiru Saminu ne ya yanke hukuncin a ranar Juma’a, 6 ga watan Nuwamba, 2026, a Babbar Kotun mai lamba 11 da ke Bompai, bayan samun mutanen biyu da laifin kisan kai a kan mutane bakwai.
Haka kuma, kotun ta yanke musu hukuncin daurin rai-da-rai tare da wahalar dauri bisa samunsu da laifin fashi da makami.
Sai dai kotun ta sallami mutum na uku, Isiyaku Abdul’azeez, wanda aka fi sani da Chebe, bayan ta bayyana cewa masu gabatar da kara sun kasa tabbatar da cewa yana da hannu a kisan ko kuma hada baki wajen aikata laifin.
Da yake jawabi bayan yanke hukuncin, Antoni Janar kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Abdulkarim Kabir Maude, ya bayyana kisan iyalan bakwai a matsayin wani mummunan lamari da ba za a taba mantawa da shi ba a tarihin jihar.
Ya ce kotun ta yi la’akari da shaidun mutane takwas da kuma kayayyakin hujja guda 30 kafin ta yanke hukuncin.
Kwamishinan ya bayyana gamsuwarsa da hukuncin, yana mai cewa gwamnatin jihar za ta tabbatar da daukar matakan da suka dace domin aiwatar da hukuncin idan wadanda aka yankewa hukuncin ba su daukaka kara cikin wa’adin da doka ta tanada ba.
Ya kuma yabawa jami’an ’yan sanda bisa gudanar da bincike mai zurfi, tare da jinjinawa ma’aikatar shari’a bisa kokarin tabbatar da an yi adalci.
A nasa bangaren, Mai shari’a Saminu ya bayyana alhininsa kan mummunan kisan, inda ya nuna cewa girman laifin ya kai matsayin da da akwai hukuncin da ya fi kisa, da kotun ta yi amfani da shi.
Tun da farko dai, an kai harin ne a ranar 17 ga watan Janairun 2026 a gidan iyalan da ke Dorayi Chiranci, inda aka kashe Fatima Abubakar da ’ya’yanta shida, yayin da mijinta, Haruna Bashir, ya tsira.
Sai dai duk da wanke Isiyaku Abdul’azeez a wannan shari’a, Antoni Janar din ya bayyana cewa har yanzu yana fuskantar wasu kararraki guda biyu da ake ci gaba da sauraro a kotu.
Tags
Labaran Duniya
