Wani sabon rahoton Bankin Duniya ya bayyana cewa ƙasar Indiya ta yi nasarar fitar da kusan mutane miliyan 500 daga kangin talauci tsakanin shekarar 2011 zuwa 2023, duk da cewa gibin da ke tsakanin masu arziki da talakawa na ci gaba da faɗaɗa.
Rahoton ya nuna cewa yawan mutanen da ke fama da matsanancin talauci a ƙasar ya ragu daga kashi 27.1 cikin 100 a shekarar 2011 zuwa kashi 2.6 cikin 100 a shekarar 2023.
Haka kuma, kimanin mutane miliyan 496 ne suka tsallake layin talauci a cikin shekaru 12, yayin da adadin mutanen da ke rayuwa da ƙasa da dala 4.20 a rana ya ragu daga kashi 57.7 zuwa kashi 16.1.
Indiya, wadda ita ce ƙasa mafi yawan al'umma a duniya da ke da kusan mutane biliyan 1.4, ta samu wannan gagarumin ci gaba sakamakon bunƙasar tattalin arziƙi, ƙarin guraben ayyukan yi musamman ga mata, da kuma faɗaɗa shirye-shiryen tallafin gwamnati.
Masana tattalin arziƙi sun danganta nasarar da wasu tsare-tsare da gwamnatocin ƙasar suka aiwatar tun bayan buɗe tattalin arziƙin ƙasar a farkon shekarun 1990.
Tsohon Firaminista Manmohan Singh ya ƙaddamar da wani shirin samar da ayyukan yi a yankunan karkara, wanda ke bai wa iyalai damar samun aikin yi na akalla kwanaki 100 a duk shekara.
Bayan hawansa mulki a shekarar 2014, Firaminista Narendra Modi ya ƙaddamar da wasu shirye-shiryen tallafi, ciki har da rabon kayan abinci kyauta, gina gidaje da kuma tura kuɗaɗen tallafi kai tsaye ga al'umma.
A halin yanzu, gwamnatin Indiya tana samar da hatsi kyauta ga kusan mutane miliyan 800.
Haka kuma, an samu ƙarin ci gaba wajen samar da ruwan sha mai tsafta a yankunan karkara, inda adadin gidajen da ke samun ruwan famfo ya karu daga ƙasa da kashi 17 cikin 100 a watan Agustan 2019 zuwa kusan kashi 82 cikin 100.
Sai dai duk da wannan nasara, masana sun nuna damuwa kan yadda gibin arziki tsakanin masu kuɗi da talakawa ke ƙara faɗaɗa a ƙasar.
Rahoton World Inequality Report na shekarar 2026 ya nuna cewa kaso 10 cikin 100 na mafiya arzikin al'ummar Indiya suna karɓar kusan kashi 58 cikin 100 na dukkan kuɗaɗen shiga na ƙasar, yayin da kaso 50 cikin 100 na mafiya talauci ke samun kashi 15 kacal.
Haka kuma, rashin aikin yi, ƙarancin albashi da kuma ƙarancin kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa wajen inganta kiwon lafiya da ilimi na daga cikin manyan ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.
Bayanan gwamnati sun nuna cewa rashin aikin yi tsakanin matasa ya ƙaru daga kashi 13.8 cikin 100 a watan Afrilun 2025 zuwa kashi 15.2 cikin 100 a watan Maris na 2026.
Wani rahoto da Jami'ar Azim Premji ta fitar ya kuma nuna cewa kusan kashi 40 cikin 100 na matasa masu digiri na jami'a masu shekaru tsakanin 15 zuwa 25 ba su da aikin yi.
Masana tattalin arziƙi sun kuma yi tambaya kan dorewar shirin raba kayan abinci kyauta ga mutane miliyan 800, suna mai cewa ya kamata gwamnati ta mayar da hankali wajen samar da ayyukan yi da inganta rayuwar jama'a maimakon dogaro da tallafi kawai.
Masanin tattalin arziƙi, Nitin Kumar Bharti, ya yaba da ci gaban da aka samu, amma ya yi gargaɗin cewa har yanzu akwai kusan mutane miliyan 233 da ke rayuwa a ƙasa da layin talauci na dala 4.20 a rana.
A nasu ɓangaren, masana sun buƙaci gwamnatin Indiya da ta ƙara zuba jari a fannin ilimi, kiwon lafiya, samar da ayyukan yi da bunƙasa yankunan karkara domin tabbatar da cewa kowa na amfana da ci gaban tattalin arziƙin ƙasar.
Sun kuma ba da shawarar amfani da tsarin haraji mai adalci, wanda zai taimaka wajen rage gibin arziki tsakanin masu hannu da shuni da sauran al'umma.
Bankin Duniya ya yi hasashen cewa talauci zai ci gaba da raguwa a Indiya a cikin shekaru masu zuwa, duk da cewa raguwar za ta kasance cikin sauri ƙasa da yadda aka gani a baya.
Duk da haka, masana sun ce rage talauci kaɗai bai wadatar ba, sai an magance matsalar rashin aikin yi da rashin daidaiton rabon arziki domin tabbatar da ingantacciyar rayuwa ga mafi yawan al'ummar ƙasar.
Tags
Labaran Duniya
