Hukumomin ƙasar China sun gurfanar da Ma Xingrui, tsohon mamba a kwamitin koli na jam’iyyar Kwaminis mai mulkin ƙasar, bisa zargin karɓar makudan kuɗaɗen cin hanci da rashawa.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasar, Xinhua, ya ruwaito cewa masu gabatar da ƙara sun zargi Ma da yin amfani da muƙaman gwamnati da kuma matsayinsa wajen samun wasu alfanu ba bisa ƙa'ida ba, tare da karɓar makudan kuɗaɗen rashawa.
Zarge-zargen sun shafi lokacin da yake riƙe da muƙaman gwamnati, da kuma tsohon aikinsa na babban manajan wani kamfanin gwamnati da ke da alhakin gudanar da shirye-shiryen binciken sararin samaniyar China.
An tabbatar da korar Ma daga jam’iyyar Kwaminis ta China a makon da ya gabata, sakamakon zarge-zargen cin hanci da rashawa da ake yi masa.
Yana cikin manyan jami’ai 33 da aka kora daga jam’iyyar, ciki har da tsohon babban jami’in soja Zhang Youxia, tsohon jami’in diflomasiyya Liu Jianchao da tsohon ministan masana’antu Jin Zhuanglong.
Wannan mataki na baya-bayan nan na nuna yadda shugaba Xi Jinping ke ƙara faɗaɗa yaƙin da yake yi da cin hanci da rashawa, musamman a tsakanin manyan jami’an gwamnati, sojoji da shugabannin siyasa.
Ya zuwa lokacin da aka fitar da rahoton, Ma bai fito fili ya mayar da martani kan zarge-zargen da ake yi masa ba, yayin da hukumomi ba su bayyana cikakken adadin kuɗaɗen da ake zargin ya karɓa ba.
Tags
Labaran Duniya
