Ƙasar Amurka ta tura Jirgin dakon Jiragen yaƙin sama na uku zuwa yankin Gabas ta Tsakiya, a daidai lokacin da rikicin da ke tsakaninta da Iran ke ƙara tsananta, lamarin da ya haifar da fargabar yiwuwar sake barkewar faɗa tsakanin ƙasashen biyu.
Jirgin dakon Jiragen yaƙin saman Amurka mai suna USS Theodore Roosevelt ya isa yankin a ranar Lahadi, 15 ga watan Nuwamba, inda ya haɗu da wasu manyan jiragen yaƙin sama guda biyu na Amurka da ke aiki a ƙarƙashin rundunar sojin Amurka ta CENTCOM.
Wani jami'in gwamnatin Amurka ne ya tabbatar da hakan a ranar Litinin, 16 ga watan Nuwamba, duk da cewa ma'aikatar tsaron ƙasar (Pentagon) da rundunar CENTCOM ba su fitar da sanarwar tabbatar da isowar jirgin a hukumance ba.
Wannan mataki na zuwa ne yayin da ƙoƙarin diflomasiyya na kawo ƙarshen yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi da Iran, tare da warware rikicin mashigar ruwa ta Hormuz, ke fuskantar matsaloli.
A baya, Amurka da Iran sun amince da tsagaita wuta na tsawon makonni biyu a watan Afrilu, kafin daga bisani su sanar da wani yarjejeniyar fahimtar juna a watan Yuni. Sai dai yarjejeniyar ta rushe a farkon watan Yuli, lamarin da ya sake jefa yankin cikin fargabar komawar faɗace-faɗace.
Tun daga lokacin ne ƙasashen Pakistan da Qatar ke ƙoƙarin shiga tsakani domin hana sake barkewar babban rikici tsakanin ɓangarorin.
A makon da ya gabata, Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa da wuya ƙasarsa ta sake kai wasu hare-haren soji kan Iran, inda ya ce, yaƙin ya kusan ƙarewa bayan tattaunawarsa da Firaministan Qatar, Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani.
Duk da haka, Trump ya jaddada cewa dakarun sojin Amurka na nan cikin shirin ko-ta-kwana idan yanayi ya sauya.
Jirgin USS Theodore Roosevelt jirgin dakon Jiragen yaƙin sama ne mai amfani da makamashin nukiliya, wanda rundunar sojin ruwan Amurka ta fara amfani da shi a shekarar 1986.
Jirgin na iya ɗaukar ma'aikata sama da 5,000, tare da jiragen yaƙi sama da 60, ciki har da jiragen F/A-18 masu kai hare-haren sama.
A baya, jirgin ya shiga wasu manyan ayyukan sojin Amurka, ciki har da Yaƙin Gulf na shekarun 1990 zuwa 1991 da kuma Yaƙin Iraki na shekarar 2003.
Isowarsa Gabas ta Tsakiya ya ƙara yawan manyan rukunonin jiragen dakon Jiragen yaƙin saman Amurka da ke yankin zuwa uku. Sauran biyun su ne USS George Washington da USS George H.W. Bush.
A wani ɓangaren kuma, Iran ta yi gargaɗi mai ƙarfi kan duk wani sabon harin soji da Amurka za ta kai mata.
Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran, Kazem Gharibabadi, ya bayyana cewa ƙasarsa ba za ta jira sai Amurka ta fara kai mata hari ba kafin ta mayar da martani.
Ya zargi Amurka da amfani da tattaunawar diflomasiyya wajen samun lokacin shirya yiwuwar sake kai hari, tare da bayyana cewa Iran na ƙara ƙarfafa ƙarfin makaman linzamin da take da su.
Haka kuma, Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya yi kira da a ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasashen yankin domin kare harkokin samar da makamashi da kuma hana ƙarin rikici.
Da yake jawabi a taron ministocin harkokin wajen ƙungiyar Economic Cooperation Organization a birnin Islamabad na Pakistan ranar Litinin, Araghchi ya yi gargaɗin cewa ci gaba da hare-haren soji da Amurka da Isra'ila ke kaiwa na iya yin barazana ga tsaron samar da makamashi a Gabas ta Tsakiya.
A ɓangaren gwamnatin Amurka kuwa, Sakataren Harkokin Waje, Marco Rubio, ya nuna cewa matakan takunkumin tattalin arziki da Amurka ke ɗauka kan Iran na yin tasiri, don haka ba lallai ba ne a sake ƙaddamar da wani gagarumin farmakin soji.
Sai dai Amurka na ci gaba da takunkumin tattalin arziki da kuma toshe hanyoyin zirga-zirgar jiragen ruwa da ke shafar kasuwancin Iran.
Iran ta sanya wasu sharuɗɗa kafin amincewa da yarjejeniyar kawo ƙarshen rikicin, ciki har da cire takunkumin hana jiragen ruwa shiga tashoshinta, da kuma ɗage takunkumin tattalin arziki da sakin kuɗaɗen ƙasar da aka ƙwace ko aka daskarar, da kuma kawo ƙarshen yaƙe-yaƙe a dukkan wuraren da ake gwabzawa.
Duk da ƙoƙarin diflomasiyya da ake yi, har yanzu ba a samu tabbatacciyar alamar cimma matsaya tsakanin ƙasashen biyu ba, sakamakon bambancin buƙatu da sharuɗɗan da kowannensu ke gabatarwa.
Masana harkokin tsaro sun yi gargaɗin cewa ƙarin ƙarfin sojin da Amurka ke tarawa a yankin, haɗe da rashin amincewa tsakanin kasashen biyu, na iya kawo cikas ga ƙoƙarin samar da zaman lafiya tare da ƙara yiwuwar sake barkewar babban yaƙi a Gabas ta Tsakiya.
Tags
Labaran Duniya
