Dan takarar jam'iyyar Democrat, Abdul El-Sayed, ya doke abokin hamayyarsa na jam'iyyar Republican, Mike Rogers, inda ya lashe zaben kujerar Majalisar Dattawan Amurka mai wakiltar jihar Michigan.
Nasarar ta sanya El-Sayed shiga tarihi a matsayin Musulmi na farko da ya taba lashe zaben kujerar Majalisar Dattawan Amurka.
El-Sayed ya samu nasarar ne a zaben tsakiyar wa'adin shugabancin Amurka da aka gudanar ranar Talata, duk da jerin hare-haren siyasa da suka shafi addininsa na Musulunci da kuma asalinsa na Larabawa, wadanda Shugaba Donald Trump da wasu 'yan jam'iyyar Republican suka rika kai masa.
Ana sa ran rantsar da shi a ranar 3 ga Janairu, 2027.
Nasarar tasa ta samu karbuwa sosai, musamman a tsakanin al'ummar Larabawa da Musulmi mazauna jihar Michigan, wadanda suka dauki zaben a matsayin wata dama ta kalubalantar wariya da nuna kyama ga mutane bisa addininsu ko asalinsu.
Babbar daraktar Cibiyar Larabawa ta Amurka (Arab American Institute), Maya Berry, ta bayyana cewa yunkurin wasu 'yan jam'iyyar Republican na amfani da kalaman kyamar Larabawa da Musulmi domin bata sunan El-Sayed bai yi nasara ba.
Ta ce nasarar tasa wata muhimmiyar alama ce da ke nuna yadda al'ummar Amurka suka yi watsi da nuna wariya da kiyayya a siyasa.
El-Sayed, wanda ya taba rike mukamin jami'in kula da harkokin lafiyar jama'a, ya mayar da hankali a yakin neman zabensa kan samar da kiwon lafiya da gwamnati za ta dauki nauyinsa ga dukkan Amurkawa, rage tasirin kudade a harkokin siyasa da kuma magance tsadar rayuwa.
Haka kuma, ya zargi Isra'ila da aikata kisan kiyashi a Gaza, tare da kira da a karkatar da kudaden da ake kashewa wajen yake-yaken kasashen waje zuwa magance matsalolin cikin gida.
A lokacin zaben fidda gwani na jam'iyyar Democrat da aka gudanar a watan Agusta, El-Sayed ya fuskanci gagarumar adawa, inda rahotanni suka nuna cewa kungiyar AIPAC ta kashe sama da dala miliyan 30 wajen yakin neman zabe a kansa.
Haka kuma, yakin neman zabensa ya kara fuskantar tangarda a kwanakin karshe bayan tsohuwar abokiyar hamayyarsa a zaben fidda gwani, 'yar majalisar wakilai Haley Stevens, ta nuna goyon bayanta ga dan takarar Republican, Mike Rogers.
Duk da wadannan kalubale, El-Sayed ya samu gagarumar goyon baya daga al'ummar Larabawa, Musulmi da kuma bakaken fata mazauna Michigan.
Shugaba Donald Trump ya sha kai masa hare-hare kan addininsa da asalinsa na Larabawa, har ma ya bayyana cewa bakaken fata da Yahudawan da suka goyi bayansa ba su da hankali.
Sai dai sakamakon farko na zaben ya nuna cewa El-Sayed ya samu gagarumar kuri'a daga bakaken fata a birnin Detroit.
Wasu masu kada kuri'a da aka zanta da su sun bayyana cewa hare-haren da aka kai wa dan takarar wani yunkuri ne na raba kan al'umma bisa bambancin launin fata da addini.
A birnin Dearborn, wanda ke da dimbin al'ummar Larabawa, wasu masu kada kuri'a sun bayyana cewa zaben ya wuce batun samun kujerar majalisar dattawa, domin a ganinsu, wani yunkuri ne na tabbatar da hakkinsu na zama cikakkun 'yan kasa da samun wakilci a Amurka.
Shugabannin al'ummar Larabawa da Musulmi sun kuma bayyana cewa hare-haren kyamar da aka kai wa El-Sayed sun kara karfafa musu gwiwar shiga harkokin siyasa da kuma kada kuri'a.
Nasarar El-Sayed ta kuma zama wata muhimmiyar nasara ga jam'iyyar Democrat, wadda ta sake samun iko da Majalisar Dattawan Amurka bayan zaben tsakiyar wa'adi.
Sai dai a wajen magoya bayansa, nasarar tasa ta fi karfin samun kujerar siyasa, domin tana nuni da kin amincewa da wariya da kyamar addini, tare da bukatar samar da shugabanci da zai bai wa kowane bangare na al'ummar Amurka dama da wakilci.
Tags
Labaran Duniya
.jpeg)