Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ƙarƙashin jagorancin Darakta-Janar ɗinsa, Sanata Abdulaziz Yari Abubakar, ya ba Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, sarautar siyasa ta ‘Kaigama’, wadda ke nufin Field Marshal, domin karrama shi bisa gudummawar da yake bayarwa ga jam’iyyar da kuma rawar da yake takawa a harkokin siyasa.
Sanata Ali Modu Sheriff, wanda yake cikin mambobin kwamitin, ne ya sanar da bayar da sarautar a yayin ziyarar da tawagar kwamitin ta kai Jihar Kebbi, a wani ɓangare na rangadin tuntubar sarakunan gargajiya a faɗin ƙasar nan gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
A cikin wata sanarwa da mai ba gwamnan shawara kan harkokin sadarwa da dabarun yaɗa labarai, Abdullahi Zuru, ya fitar ranar Talata, ya bayyana cewa an karrama Gwamna Idris ne bisa jajircewarsa ga APC, ƙwazonsa wajen gudanar da mulki da kuma ƙoƙarinsa na ƙarfafa goyon bayan siyasa ga jam’iyyar.
Tawagar, wadda Sanata Yari ya jagoranta, ta ziyarci Sarkin Gwandu, kuma shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Jihar Kebbi, Alhaji Muhammadu Bashar, domin gaishe shi tare da neman addu’o’insa da fatan alheri gabanin fara harkokin yaƙin neman zaɓe.
An tarbi tawagar a filin jirgin saman Ahmadu Bello da ke Birnin Kebbi, inda Gwamna Nasir Idris ya jagoranci ɗimbin jama’a wajen tarbar baƙin. Daga nan ne aka ci gaba da tarbar a fadar Sarkin Gwandu, inda ’yan kasuwa, manoma, masu rawa ta gargajiya da mawaƙan yabo suka halarta.
Sauran sarakunan da suka halarci taron sun haɗa da Sarkin Argungu, Alhaji Samaila Mera; Sarkin Yauri, Dakta Zayyanu Abdullahi; da Sarkin Zuru, Alhaji Muhammad Gomo III.
Da yake jawabi a yayin ziyarar, Sanata Yari ya ce sun zo ne domin girmama Sarkin Gwandu tare da neman addu’a da shawarwari kafin fara yaƙin neman zaɓe.
A nasa martanin, Sarkin Gwandu ya gode wa tawagar bisa ziyarar, sannan ya buƙaci ’yan siyasa da su tabbatar da gudanar da yaƙin neman zaɓe cikin lumana gabanin zaɓukan shekarar 2027.
A fadar gwamnatin jihar da ke Birnin Kebbi, Sanata Yari ya bayyana jin daɗinsa bisa irin tarbar da aka yi musu, yana mai cewa tarbar ta kasance ta musamman kuma ita ce mafi girma tun bayan fara rangadin ziyarar sarakunan gargajiya da kwamitin ke yi a faɗin ƙasar nan.
Ya danganta ƙarfin siyasar APC a Jihar Kebbi da shugabancin Gwamna Nasir Idris, inda ya bayyana gwamnan a matsayin ɗaya daga cikin manyan ginshiƙan da suka taimaka wajen ƙarfafa matsayin jam’iyyar a jihar.
Haka kuma, Sanata Yari ya yabawa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa ayyukan da gwamnatin ta gudanar cikin shekaru uku da suka gabata sun ba da dalilin da ya sa wasu ke kira da a sake zaɓen shugaban ƙasar a shekarar 2027.
A nasa jawabin, Gwamna Nasir Idris ya danganta ƙarfin APC a Kebbi da gudummawar manyan jagororin jam’iyyar da sauran masu ruwa da tsaki, ciki har da tsohon gwamnan jihar kuma Sanata, Adamu Aliero; Ministan Tsare-tsaren Kasafin Kuɗi da Tattalin Arziki, Atiku Bagudu; tsohon Gwamna Sa’idu Nasamu Dakingari; da Sanata Yahaya Abdullahi.
Gwamnan ya kuma ce ayyukan raya ƙasa da gwamnatinsa ta aiwatar sun taimaka wajen sauya alkiblar ci gaban jihar tare da ƙara wa jam’iyyar farin jini a tsakanin al’umma.
Idris ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa ziyarar yaƙin neman zaɓen APC da za a kai jihar nan gaba za ta kasance mai sauƙi, yana mai cewa al’ummar jihar sun riga sun fara nuna sha’awarsu ga babban zaɓen 2027.
Sanata Ali Modu Sheriff ne ya sanar da bayar da sarautar ‘Kaigama’ ga gwamnan a yayin taron, bisa amincewar shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓen. Matakin ya kasance wata alama ta karrama gwamnan bisa jajircewarsa da ƙoƙarinsa na ƙarfafa APC a Jihar Kebbi.
Tags
Labaran Duniya
