Gwamnatin Iran ta sake jaddada aniyarta ta bin hanyoyin diflomasiyya domin kawo ƙarshen yaƙin da take yi da Amurka da Isra’ila, amma ta bayyana cewa a shirye take ta kare kanta daga duk wani sabon hari.
Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ne ya bayyana hakan a cikin wata makala da aka wallafa a jaridar Financial Times, inda ya ce ƙasarsa na da cikakken burin cimma matsaya ta lumana da za ta kawo ƙarshen rikicin.
Araghchi ya ce duk da aniyar Iran ta neman zaman lafiya, ƙasar ba za ta yi ƙasa a gwiwa wajen kare kanta ba idan aka kai mata hari.
Ya kuma zargi Fadar White House da rashin nuna cikakkiyar niyya ta cimma matsaya da Tehran, yana mai cewa akwai ƙarancin alamun samun ci gaba a tattaunawar sulhu a halin yanzu.
Amurka Ta Ce Cimma Yarjejeniyar Sulhu Da Iran Zai Yi Wuya
Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya bayyana cewa cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Iran abu ne mai matuƙar wahala.
Rubio ya ce Amurka za ta ci gaba da matsin tattalin arziki a kan Iran har sai ta dakatar da hare-haren da take kai wa jiragen kasuwanci a mashigar ruwan Hormuz.
Mashigar ruwan Hormuz na ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin jigilar makamashi a duniya, inda ake safarar ɗanyen mai da sauran kayayyakin makamashi zuwa kasuwannin duniya.
Rikicin da ya shafi wannan mashigar ruwa na ci gaba da zama ɗaya daga cikin manyan matsalolin da ke kawo cikas ga ƙoƙarin rage tashin hankali tsakanin Amurka da Iran.
Shi ma Shugaban Ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya soki yadda Amurka ke tafiyar da lamarin, yana mai cewa Amurka ba za ta iya tsammanin samun tattaunawa mai ma’ana da Iran ba yayin da take ci gaba da killace ƙasar tare da yi mata barazana.
A cewar rahotannin kafafen yaɗa labaran gwamnatin Iran, Pezeshkian ya ce dole ne Amurka ta amince da haƙƙoƙin al'ummar Iran tare da dakatar da abin da ya kira zalunci da barazana kafin a iya komawa teburin tattaunawa.
Ya kuma zargi Amurka da rashin cika yarjejeniyoyin dake tsakaninsu, yana mai jaddada cewa ya kamata ƙasashe su mutunta yarjejeniyoyin da suka kulla har zuwa ƙarshe, ko da kuwa hakan zai iya zama ba daidai da muradunsu ba.
Tags
Labaran Duniya
