Harin Jirgin Sama Marar Matuki Ya Hallaka Mutane 153 a Kasuwar Abyei dake iyakar Sudan da Sudan ta Kudu.

Harin Jirgin Sama Marar Matuki Ya Hallaka Mutane 153 a Kasuwar Abyei dake iyakar Sudan da Sudan ta Kudu.

Akalla mutane 153 ne suka mutu sakamakon wani harin jirgin sama marar matuki da aka kai wata kasuwa da ke yankin Abyei, wanda ake takaddama a kansa tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu.

Wani jami’in gwamnatin yankin Abyei ne ya bayyana adadin waÉ—anda suka mutu, inda ya ce ana fargabar adadin zai Æ™aru yayin da ake ci gaba da tantance waÉ—anda harin ya rutsa da su.

Harin ya faru ne a ranar Litinin, 19 ga Oktoba, a kasuwar Amiet, da ke arewacin garin Abyei.

Mukaddashin ministan yaɗa labarai na gwamnatin yankin Abyei, Yohanna Akol Ngor, ya ce har yanzu gobara na ci gaba da ci a wurin da harin ya afku, yayin da wasu gawarwakin waɗanda suka mutu suka ƙone matuƙa.

Ngor ya bayyana halin da ake ciki a matsayin abin ban tsoro, yana mai cewa ana sa ran adadin waɗanda suka mutu zai ƙaru.

Sudan ta Kudu Ta Zargi Sojojin Sudan

Hukumomin Sudan ta Kudu sun zargi sojojin Sudan da kai harin, inda suka ce jiragen sama marasa matuƙi sun farmaki wurare da dama a cikin kasuwar.

Ma’aikatar Harkokin Waje da HaÉ—in Kan Ƙasa ta Sudan ta Kudu ta bayyana rashin amincewarta da harin, tare da kiran jakadan Sudan domin yi masa bayani kan lamarin.

Haka kuma, ta buƙaci Sudan da ta guji duk wani mataki da zai jefa rayukan fararen hula da dukiyoyinsu cikin haɗari.

Sai dai, rundunar sojin Sudan ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan zargin ba har zuwa lokacin haÉ—a wannan rahoto.

Wani babban jami’in sojin Sudan, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press cewa sojojin sun kai hari kan motocin dakon mai da ke shigowa daga Sudan ta Kudu, waÉ—anda ake zargin suna kai mai ga dakarun Æ™ungiyar Rapid Support Forces (RSF).

Jami’in ya yi iÆ™irarin cewa waÉ—anda suka mutu mambobin RSF ne da masu safarar mai ba bisa Æ™a’ida ba, yana mai jaddada cewa sojojin Sudan ba sa kai hari da gangan kan fararen hula.

A gefe guda kuma, wasu jami’an diflomasiyya da suka yi magana da kamfanin dillancin labarai na Reuters sun ce harin ya faÉ—a kan wata matatar ajiye mai da ke cikin kasuwar, wadda RSF ta taÉ“a amfani da ita wajen samar wa dakarunta mai.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ƙungiyar RSF ba ta fitar da wata sanarwa kan harin ba.

Majalisar ÆŠinkin Duniya Ta Yi Allah-Wadai da Hare-Haren

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi Allah-wadai da hare-haren jiragen sama marasa matuƙi da aka kai kusa da kasuwar Amiet da yankin Todach.

Mai magana da yawun babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Stéphane Dujarric, ya ce hare-haren sun yi sanadin mutuwar fararen hula da dama, ciki har da mata da yara, tare da jikkata wasu da dama.

Majalisar ta bayyana cewa har yanzu akwai mutanen da ba a san inda suke ba, yayin da ake fargabar adadin waɗanda suka mutu zai ƙaru.

Rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar ÆŠinkin Duniya a Abyei (UNISFA) na ci gaba da tantance adadin waÉ—anda suka mutu da waÉ—anda suka jikkata.

A nata ɓangaren, ƙungiyar agaji ta likitoci ta Doctors Without Borders (MSF) ta ce tana kula da sama da mutum 20 da suka jikkata sakamakon harin, inda wasu daga cikinsu suka samu munanan ƙonewa.

Yaƙin Sudan Na Ƙara Ta'azzara Matsalar Jin Ƙai

Harin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da yaƙi tsakanin sojojin gwamnatin Sudan da dakarun RSF, wanda ya ɓarke a watan Afrilun 2023.

Yaƙin ya haddasa mummunar matsalar jin ƙai a Sudan, inda fararen hula da dama ke fuskantar barazanar rasa rayukansu, matsugunansu da hanyoyin samun abinci da sauran muhimman buƙatu.

Duk da cewa Sudan ta Kudu ta bayyana cewa ba ta goyon bayan wani É“angare a rikicin, wasu jami’an diflomasiyya sun ce yankin Abyei ya zama muhimmiyar hanyar da ake bi wajen kai mai ga dakarun RSF.

Abyei yanki ne mai arzikin albarkatun ƙasa, wanda Sudan da Sudan ta Kudu suke ikirarin mallakarsa. Yankin na ƙarƙashin tsarin gudanarwa na haɗin gwiwa tun bayan da Sudan ta Kudu ta samu 'yancin kai a shekarar 2011.

Yankin yana iyaka da Kordofan, wani yanki na Sudan da ya zama ɗaya daga cikin manyan wuraren da ake gwabza faɗa a yaƙin da ke ci gaba da addabar ƙasar.

Harin na baya-bayan nan ya ƙara tayar da hankalin al'ummar duniya kan tsaron fararen hula a yankunan da ke kan iyakar ƙasashen biyu, yayin da hare-haren jiragen sama marasa matuƙi ke ƙara yaɗuwa a Sudan.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Contact Form