An Tsige Limamin Masallaci a Bauchi Bisa Zargin Yiwa Tinubu Kamfen

An Tsige Limamin Masallaci a Bauchi Bisa Zargin Yiwa Tinubu Kamfen

An tsige Limamin wani masallaci da ke unguwar Madina a cikin birnin Bauchi, mai suna Dahiru Abubakar, daga mukaminsa bisa zargin amfani da wa'azinsa wajen yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kamfen gabanin zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Rahotanni sun nuna cewa limamin ya sha bayyana goyon bayansa ga sake zaɓen Tinubu yayin wa'azinsa ga jama'a bayan kammala sallolin farilla.

An ce matakin tsige shi ya biyo bayan sake maimaita wannan al'amari bayan sallar Asuba a ranar Lahadi, inda ake zargin ya shaida wa masu ibada cewa Tinubu ba shi ne ya haddasa matsalar rashin tsaro ba, kuma ya cancanci a sake zaɓensa.


Da yake bayyana dalilin wa'azinsa, Abubakar ya ce yana ƙoƙarin wayar da kan al'umma ne domin su daina ɗora wa Shugaba Tinubu alhakin matsalolin tsaro da ƙuncin tattalin arziki da ƙasar ke fuskanta.

Ya bayyana cewa matsalar rashin tsaro ba ta taƙaita ga Najeriya kaɗai ba, domin akwai ƙasashen Afirka kamar Sudan, Chadi da Mali da su ma ke fuskantar irin waɗannan matsaloli.

Limamin ya ce saƙon da yake isarwa ga jama'a ya ta'allaka ne kan tsoron Allah, kyautata rayuwar yau da kullum da kuma yin addu'a domin samun mafita daga ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.

Ya kuma bayyana cewa yana ƙarfafa mutane su bai wa Tinubu wata dama ta sake jagorantar Najeriya bayan zaɓen 2027.

Sai dai shugaban kwamitin gudanarwar masallacin, Imam Abubakar Jibrin, ya ce ba wai goyon bayan Tinubu kaÉ—ai ne ya jawo tsige limamin ba, har ma da yadda ake zarginsa da mayar da masallacin wajen gudanar da harkokin siyasa.

Jibrin ya bayyana cewa kwamitin ya sha gargaÉ—in Abubakar kan amfani da masallacin wajen tattauna siyasa da kuma tara jama'a domin gudanar da ayyukan siyasa.

Ya jaddada cewa duk da muhimmancin siyasa wajen zaɓar shugabannin ƙasa, ya kamata a gudanar da kamfe da tarukan siyasa a ofisoshin jam'iyyun siyasa, ba a cikin masallatai ba.

Shugaban kwamitin ya kuma zargi limamin da dagewa kan sauya sunan masallacin daga Masjid Abdullahi Bin Zubbair zuwa Masjid Imam Bola Ahmed Tinubu.

A cewarsa, kwamitin ya ƙi amincewa da wannan buƙata saboda masallacin mallakin al'umma ne, don haka ba mutum ɗaya ne zai sauya masa suna bisa ra'ayinsa ba.

Jibrin ya ce kwamitin ya yanke shawarar ci gaba da amfani da sunan masallacin na asali, tare da tabbatar da cewa ba za a mayar da Abubakar kan mukaminsa na limanci ba.

Ya ƙara da cewa mambobin kwamitin ba sa adawa da Tinubu ko wani ɗan takarar siyasa, sai dai suna ganin ya kamata masallaci ya kasance wurin bautar Allah, ba wajen gudanar da harkokin siyasa ba.

Ya bayyana cewa abin da kwamitin ke buƙata shi ne al'umma su roƙi Allah Ya zaɓa musu shugaba nagari wanda zai zama alheri ga Najeriya, ko wanene ɗan takarar da zai samu nasarar shugabantar ƙasar.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Contact Form