Thursday, September 24, 2026

Tsohon Kyaftin ɗin Super Eagles William Troost-Ekong Ya Musulunta

Tsohon Kyaftin ɗin Super Eagles William Troost-Ekong Ya Musulunta

Tsohon kyaftin ɗin tawagar Super Eagles ta Najeriya, William Troost-Ekong, ya musulunta.

Rahotanni sun ce ɗan wasan mai shekaru 33 ya karɓi Musulunci ne bayan ya furta Kalmar Shahada a birnin Doha na ƙasar Qatar, inda yake taka leda a ƙungiyar Al-Ahli ta Qatar Stars League.

Jaridar Qatar mai suna Al-Arab ce ta wallafa rahoton a ranar Laraba. Haka kuma, fitaccen malamin addinin Musulunci, Dr Muhammad Salah, ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na Facebook da aka tabbatar, inda aka ga Troost-Ekong yana furta Kalmar Shahada.

Troost-Ekong ya koma yankin Gabas ta Tsakiya a shekarar 2024, bayan ya rattaba hannu da ƙungiyar Al-Khaleej ta Saudiyya.

A watan Janairun 2026, ya koma Al-Ahli ta Qatar kan yarjejeniyar shekara ɗaya da rabi. Tun bayan komawarsa ƙungiyar, ya buga wasanni 14 a dukkanin gasanni, ciki har da wasa ɗaya a kakar bana.

A matakin ƙasa da ƙasa, Troost-Ekong ya wakilci Najeriya daga shekarar 2015 zuwa 2025, inda ya buga wasanni 83 tare da zura ƙwallaye takwas.

Ya kasance cikin tawagar Super Eagles da ta kai wasan ƙarshe na gasar AFCON 2023 da aka gudanar a Côte d’Ivoire, inda aka zaɓe shi a matsayin gwarzon ɗan wasa na gasar.

Haka kuma, Troost-Ekong ya wakilci Najeriya a gasar Kofin Duniya ta FIFA da kuma wasannin Olympics, inda ya kasance ɗaya daga cikin ƙwararrun masu tsaron baya da suka yi fice a tarihin Super Eagles a cikin shekaru goma da suka gabata.

0 Comment about the Post: