Mutane 12 ne Suka Rasa Rayukansu a Wani Harin Bam a Arewa maso Yammacin ƙasar Pakistan.

Mutane 12 ne Suka Rasa Rayukansu a Wani Harin Bam a Arewa maso Yammacin ƙasar Pakistan.

Akalla mutane 12 ne, ciki har da mata biyu da yara biyu, suka mutu yayin da wasu 18 suka jikkata a wani harin kunar bakin wake da aka kai kan ofishin binciken ‘yan sanda a arewa maso yammacin Pakistan.

Harin ya faru ne a ranar Asabar, 26 ga Satumba, 2026, a yankin Darazinda da ke gundumar Dera Ismail Khan, kusa da iyakar jihohin Khyber Pakhtunkhwa da Balochistan.

A cewar ‘yan sanda, dan kunar bakin waken da ake zargin yana cikin kungiyar Tehreek-e-Taliban Pakistan (TTP), wadda gwamnati ta haramta, ya tuka wata tirela mai dauke da abubuwan fashewa ya kutsa da ita cikin shingen binciken ‘yan sanda na Aman Mela.

Jami’in ‘yan sandan yankin, Khan Mubashir Malik, ya tabbatar da mutuwar mutane 12 da jikkatar wasu 18. 
Ya ce jami’ai biyu daga hukumar Kwastam da Haraji na cikin wadanda harin ya kashe.

An garzaya da wadanda suka jikkata zuwa Asibitin Kwararru na Gundumar domin samun magani, yayin da aka kai gawarwakin wadanda suka mutu zuwa asibitin.

Kungiyoyin kwararru kan kwance bama-bamai sun isa wurin domin gano nau’in abubuwan fashewar da aka yi amfani da su. 
Hukumomin tsaro kuma sun killace yankin tare da fara gudanar da bincike da samame bayan harin.

Jihar Khyber Pakhtunkhwa ta sha fuskantar hare-haren kungiyoyin mayaka a shekarun baya-bayan nan, musamman sakamakon ayyukan kungiyoyin dake dauke da makamai da kuma kutsen mayaka daga Afghanistan.

Gwamnatin tarayyar Pakistan ta dade tana zargin kungiyar TTP da kai hare-hare a jihar tun bayan da kungiyar ta kawo karshen yarjejeniyar tsagaita bude wuta da gwamnati a watan Nuwamban 2022.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Contact Form