Tuesday, August 11, 2026

An Kashe Shugaban Leken Asirin Sojin Gabashin Libya a Harin Bam a Mota.

An Kashe Shugaban Leken Asirin Sojin Gabashin Libya a Harin Bam a Mota.

An kashe Manjo-Janar Fawzi al-Mansouri, shugaban hukumar leken asirin soji ta rundunar da ke iko da gabashin ƙasar Libya, bayan da aka kai masa harin bam a birnin Benghazi.

Rahotanni sun ce an dasa wata na’urar fashewa a cikin motarsa, inda aka tayar da ita yayin da al-Mansouri ke shiga motarsa a wajen gidansa da ke yankin Hawari a daren ranar Litinin.

Firaministan gwamnatin gabashin Libya, Osama Saad Hammad, ya yi Allah-wadai da kisan tare da yin alkawarin gudanar da bincike domin gano wadanda suka shirya da kuma wadanda suka aikata harin.

Hammad ya bayyana harin a matsayin “mummunan aikin ta’addanci da cin amana”, yana mai cewa ba za a bar wani mutum ya samu mafaka ba idan yana da hannu wajen tsarawa ko aiwatarwa ko daukar nauyin kudi ko kuma tunzura ayyukan kisan gilla da ta’addanci.

An nada al-Mansouri a matsayin daraktan leken asirin soji a Benghazi a shekarar 2024, tare da ba shi mukamin Manjo-Janar.

Kisan na zuwa ne yayin da Libya ke ci gaba da fama da rikicin siyasa da matsalolin tsaro, inda gwamnatoci masu hamayya da kungiyoyin masu dauke da makamai ke ci gaba da samun tasiri duk da yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta shekarar 2020.

Libya ta rabu gida biyu tun daga shekarar 2014, bayan rikicin siyasa da na soji da ya biyo bayan juyin mulkin shekarar 2011 wanda ya kifar da mulkin tsohon shugaban kasar Muammar Gaddafi.

Rundunar LNA karkashin jagorancin Khalifa Haftar ce ke iko da manyan sassan gabashi da kudancin Libya, kuma tana da alaka da hukumomin da ke birnin Benghazi.

A gefe guda kuma, gwamnatin hadin kan kasa da duniya ke amince da ita, wadda ke da hedikwata a Tripoli, ita ce ke iko da mafi yawan yankunan yammacin kasar.

Kisan babban jami’in leken asirin sojin ya kara jefa haske kan matsalolin tsaro da Libya ke fuskanta, tare da haifar da sabbin damuwa game da makomar zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

0 Comment about the Post: