Laylatul Qadr dare ne mai girma da albarka a cikin watan Ramadan, wanda Allah Ya fifita shi fiye da sauran darare. A cikin Surah Al-Qadr, Allah Ya bayyana cewa ibadar da aka yi a wannan dare ta fi ta watanni dubu lada.
Musulmai na neman wannan dare ne a cikin dararen goma na ƙarshe na Ramadan, musamman a ranakun mara. A wannan lokaci ne ake ƙara ƙoƙari wajen ibada domin samun rahamar Allah da gafararSa.
Annabi Muhammad ya ƙarfafa wa Musulmai gwiwa su raya wannan dare da ayyukan ibada kamar:
Yin sallar dare (Tahajjud ko Qiyamul-Lail)
Karatun Alƙur’ani
Yawaita zikiri da istighfari
Yin addu’o’i da neman gafarar Allah
Bayar da sadaka da aikata alheri
Daga cikin addu’o’in da Annabi ya koyar a riƙa yi a wannan dare akwai:
“Allahumma innaka ‘afuwwun tuhibbul ‘afwa fa’fu ‘anni,” wato: Ya Allah Kai Mai gafara ne, kana son gafara, ka gafarta mini.
Lailatul Qadri dare ne na rahama, albarka da gafarar zunubai. Saboda haka, ya dace Musulmai su ƙara himma wajen ibada a dararen ƙarshe na Ramadan domin samun wannan falala mai girma.
Article Translation in English Language.
Laylatul Qadr: The Most Blessed Night in Ramadan
Laylatul Qadr is a highly blessed and significant night during the holy month of Ramadan, which Allah has given special virtue above other nights. In Surah Al-Qadr, Allah states that worship performed on this night is better than that of one thousand months.
Muslims seek this special night during the last ten nights of Ramadan, particularly on the odd-numbered nights. During this period, believers increase their acts of worship in the hope of attaining Allah’s mercy and forgiveness.
The Prophet Muhammad encouraged Muslims to spend this night in devotion through acts such as:
Performing night prayers (Tahajjud or Qiyam al-Layl)
Reciting the Qur’an
Engaging in remembrance of Allah (dhikr) and seeking forgiveness (istighfar)
Making sincere supplications (du’a)
Giving charity and doing good deeds
One of the supplications the Prophet recommended for this night is:
“Allahumma innaka ‘afuwwun tuhibbul ‘afwa fa’fu ‘anni,”
meaning: O Allah, You are Most Forgiving and You love forgiveness, so forgive me.
Laylatul Qadr is a night filled with mercy, blessings, and forgiveness. Therefore, Muslims are encouraged to increase their worship during the last nights of Ramadan in order to attain the immense rewards and blessings of this sacred night. ✨

0 Comment about the Post: