Tuesday, November 18, 2025

Wasu daga cikin Dabi'u da siffofin Manzon Allah (S.A.W)

Wasu daga cikin Dabi'u da siffofin Manzon Allah (S.A.W)

Hakika manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare ya kasance abun koyi ga dukkan musulmi da duniya baki daya ta fuskar mu'amala da mutane da bayyana soyayya ga raunana da nuna jinkai ga dukkan hakiittan ubangiji.

Ga jerin wasu daga cikin Dabi'u da siffofin fiyayyen Halitta ANNABI MUHAMMAD Sallallahu Alaihiwasallam.

1. Idanun Manzan Allah (ﷺ) sun kasance masu yawan zubar da hawaye na tsoron Allah (SWT).

2. Dariyar Shugaba (ﷺ) shine murmushi baya kyakyatawa, yafi mutane yawan murmushi (ﷺ).

3. Baya cin abinci mai zafi yana cewa abinci mai zafi bashi da albarka. 

4. Idan aka kawo masa abinci na gaban sa yake ci baya kai hanun sa wani wajen daban.

5. Abinda yafi so daga abinci shine; nama, kuma yana son gurji/kwakwamba, yana cin naman kaza da naman tsuntsaye da aka farauto.

6. Yana son kabewa, amma baya cin albasa/tafarnuwa da algaragis (amma be haramta ba).

7. Ya kasance (ﷺ) yana da mudubi da kum na taje kai da kuma aswaki ko yaushe yana tare dasu saboda tsaftar sa da kuma gayun sa.

8. Idan yana shan ruwa (ﷺ) baya numfashi a cikin ƙwaryar da yake sha, sai dai ya cire kansa idan yayi numfashi sai ya cigaba da sha.

9. Be hana a saka kowane kala daga tufafi ba sai da yaƙiwa sahabban sa su sanya jajayen kaya zalla babu ratsin wata kalar a jiki.

10. Shugaba (ﷺ) ya kasance yana da wando, kuma yana sanya zobe, sai dai amma idan ya sanya zoben yana juyo kan zoben ya kalli ƙasa ma'ana ya juyo ta cikin tafin sa.

11. Annabi (ﷺ) yana sanya hula sai ya sanya rawani a samanta.

Allah (SWT) ya ƙara masa tsira da aminci...

Indai ANNABI nada matsayi agunka Katura group's 5

👇👉👇👉👉https://www.facebook.com/share/g/1CKc8iYeoK/

SHARE THIS

Author:

I am a personal blogger by experience, interesting in creativity, learning new things and sharing Islamic contents for the benefit of Muslim ummah.

0 comments: