Manzon Allah (S.A.W) shine mafi cikar Kyawawan Siffofi da halaye a duk cikin Halittun Allah (S.W.T). Don haka ya zama mafifici acikinsu.
Hakika wadannan halayen nasa, girmansu ya kai girma. Tunda har Ubangiji da kanShi ya yabe Shi akansu. Yana cewa:
"KUMA HAKIKA KAI WALLAHI KANA BISA WASU DABI'O'I MASU GIRMA".
Wadannan dabi'o'in na Manzon Allah (saww) sune ainihin tushen Musulunci, Dasu ake samun cikar Imani da kuma Kusanci zuwa ga Allah da Manzonsa.
Manzon Allah (saww) yace: "BABU ABINDA YAFI SHIGAR DA MUTANE CIKIN ALJANNAH KAMAR TSORON ALLAH DA KUMA KYAWUN HALAYE".
Kuma yace: "BABU ABINDA YAFI NAUYAYA MIZANIN MUTUM ARANAR ALKIYAMAH FIYE DA KYAWAWAN DABI'U".
Idan kana koyi da ayyukan Manzon Allah (S.A.W) kadai, amma ka watsar da yin koyi da Halayensa, to tabbas zaka tashi akarkashin tutar Munafurci.
Kuma ba zaka samu komai awajen Allah ba.
Lalla ne duk mai neman rabauta a duniya da lahira ya rike koyi da Halayen Manzon Allah (S.A.W) da kuma ayyukansa.
Wannan shine cikakken mai bin Sunnah.
Yana daga cikin irin halayen nan nasa:
1. Kiyaye harshenka daga chutar da Musulmai har da ma wadanda ba musulmai ba.
2. Kyautata wa Makiyinka kamar yadda zaka kyautata wa masoyinka.
3. Yafewa da yin afuwa ga mutumin da ya zalunceka, koda kana da cikakkiyar damar daukar matakin ramuwa.
4. Kaskantar da kanka ga bayin Allah. Koda ka girmesu, koda ka fisu Ilimi ko dukiya ko Mulki ko daukaka.
5. Son Miskinai da fakirai da Marayu, da sauran marassa Qarfi. tare da tsayawa akan bukatunsu ba tare da nuna gazawa ba.
6. Rike zumunta tsakaninka da 'yan uwanka tare da kyautata musu koda su suna munana maka.
7. Tsayuwa akan gaskiya ko yaushe tare da rikon amanar Jama'a. Da kuma kyautata zato ga Allah da bayinsa.
Allah shi Qara mana son Manzon Allah (S.A.W) tare da riko gamgam bisa sunnarsa da girmamashi a koda yaushe.
Allah madaukakin sarki yasa mu dace.
_1.jpeg)